A biya naira miliyan 200 ko mu kashe dan sandan da muka sace – Yan bindiga

‘Yan bindiga sun bukaci a biya su Naira miliyan 200 kafin su saki dan sandan dake gadin marigayi Sagir Hamida da suka sace bayan sun kashe Sagir Hamida.

Sunan dan sandan Sambo Hosea kuma ‘yan bindigan sun bukaci iyalan Hosea su yi gaggawar aiko da naira miliyan 200 tun suna inda za a same su a waya wurin da akwai sabis.

A wani rikodin din maganar da aka yi tsakanin ‘yan bindigan da iyalan Hosea da wakilin PREMIUM TIMES ya saurara ‘yan bindigan sun fusata a lokacin da iyalin Hosea suka ce Naira miliyan biyu ne suka iya hadawa.

“Mun baku awa 6 ku hada mana wadannan kudade idan ba haka ba dan uwan ku zai sha dukan tsiya sannan kuma za mu kashe shi.

Shima Hosea ya roki ‘yan uwan sa da su yi kokari su hada kudaden domin a sake shi.

Ya ce sai da suka yi tafiya mai nisa wajen samo sabis.

“Ku yi kokari ku hada kudaden nan ko da babu a ara idan na dawo zan biya domin halin da nake ciki babu kyau. Inji Hosea.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Hosea da wasu mutane da dama bayan sun kashe tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara a zaben 2019, Sagir Hamida a titin Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishina ‘yan sandan jihar Kaduna Abdullahi Mudassiru ya ce ‘yan sanda tare da hadin guiwar sojoji sun ceto mutum 11 daga ciki har da gawar marigayi Hamida a kauyen Kurmin kare, dake iyaka da Titin.

Kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro wajen ganin an kawo karshen hare-hare da ake kaiwa matafiya a wannan titi.

Hakazalika ya yi kira ga matafiya da su rika hakuri a lokacin da suke tafiya, su daina bin hannun da ba nasu ba domin hakan na sa a rika samun hadarurruka da kuma cunkoso a hanyar ta inda zai sa mugayen mutane su kawo wa matafiya hari.