2023: Yadda zan kawo ƙarshen masu neman kafa Biafra – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023 mai zuwa z Atiku Abubakar, ya bayyana cewa masu neman kafa Biafra na yi ne saboda ganin cewa su an mayar da su saniyar-ware a harkokin mulkin Najeriya.
Don haka sai Atiku ya tabbatar da cewa shi zai magance masu wannan miki da ƙarƙashin da ke damun zukatan su idan ya zama shugaban ƙasa.
Ya ce neman kafa Biafra a yankin Kudu maso Gabas zai zama tarihi, kamar yadda ya bayyana taron shugabannin PDP na yanzu Kudu maso Gabas da aka yi a Enugu.
An shirya taron e da nufin haɗa kan ƙabilar Igbo su zaɓi PDP, tare da gabatar masu da Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, mai wa Atiku takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Atiku ya ce ajandar sa ita ce ceto Najeriya, gagarimin aikin da zai amfani yankin Kudu maso Gabas sosai da sauran yankuna baki ɗaya.
Idan ba a manta ba, lokacin da Atiku ya bayyana Okowa a matsayin mataimakin takarar sa, ya yi alƙawarin cewa idan ya zama shugaban ƙasa, to mataimakin sa ne zai gaje shi idan ya sauka.
Hakan na nufin Okowa zai zama mai jiran gado kenan idan har Atiku Abubakar ya yi nasara a zaɓen 2023.
“Dole mu kawo karshen abin da ke sa wasu ke kallon an maida su saniyar-ware. Kuma wannan ne ke sa su na kafa hujjar su ta neman ɓallewa,” inji Atiku.
Tun daga 1999 Kudu maso Gabas ke ƙorafin an maida su saniyar-ware, musamman an hana su damar yin shugabancin ƙasa.
Wannan lamarin ne ya haifar da taratsin Nnamdi Kano, har abin ya kai ga mamaye jihohin Kudu maso Gabas baki ɗaya.