2023: Tinubu ya garzaya Landan, amma zai dawo dab da fara Kamfen

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC ya tafi Landan a ranar Litinin, kwanaki kaɗan kafin ya fara kamfen ɗin yaƙin neman zaɓe.
Majiya daga cikin APC ta tabbatar da cewa Tinubu ya je Landan ne domin ganawa da wani gungun mutane. Sai dai kuma ba a bayyana sunayen mutanen ba.
PREMIUM TIMES ta gano cewa tun a ƙarshen makon nan Tinubu ya kamata ya tafi, to amma ya jinkirta tafiyar ce saboda hayaniyar da ta taso daga ɓangaren gwamnoni bayan fitar da jadawalin sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu su 422, wanda bai yi wa gwamnonin daɗi ba.
Akwai masu hasashen cewa Tinubu ya tafi Landan ne domin ya gana da Gwamna Nyesom Wike da rundunar sa a can, ganin cewa yanzu haka Wike ya na Landan tun ranar Asabar shi da wasu makusantan sa.
Haka kuma akwai masu cewa Tinubu ya tafi ne domin yi wa jiki garambawul, domin a cikin wannan makon APC za ta fara kamfen a garin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Ana buƙatar ganin Tinubu a dukkan jihohin da APC za ta je kamfen.
A ranar 28 ga Satumba za a fara kamfen na zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dattawa da ta Tarayya.
Za a fara kamfen na zaɓen gwamna a ranar 12 Ga Oktoba.