2023: Takarar ‘Muslim-Muslim’ rashin adalci ne, ƙara rura ƙiyayya da ƙara nesanta haɗin kan ‘yan Najeriya ne -Hassan Kukah

Babban Limamin Kiristoci Mathew Hassan-Kukah, ya bayyana cewa takarar ‘Muslim-Muslim’ wadda APC ta tsayar da Bola Tinubu da Kashin Shettima takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa, rashin adalci ne tantagarya wanda shi dai zuciyar sa ba za ta taɓa amincewa da shi ba.
Da ake tattaunawa da shi a filin ‘Siyasa a Yau’ na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Alhamis, Kukah ya ce APC ba ta damu da duban yanayin da al’ummar Najeriya za su ji ba da kuma duban abin da ya kamata, “duk da shekarun da jam’iyyar ta ɓata a banza bayan an ba ta damar da ta nema a 2015.”
Ya ce masu bada misali da cewa ai ba wani abu ba ne, tunda a 1993 ma an taɓa yin haka, Kukah ya ce wannan rashin tunani ne matuƙa.
“Ya kamata masu wannan misalin su tuna cewa a 1993 fa lokacin sojoji ake so a kora daga mulki kawai, don haka ko ma ta wace hanya dai an bi. Amma yanzu bayan shekaru da yawa, bai yiwuwa ‘yan siyasa su yi watsi da buƙatar mabiya wani addini don kawai su daɗaɗa wa son ran su.”
“A 1984 kuma (lokacin da Buhari da mataimakin sa Tunde Idiagbon duk Musulmai ne) mulkin soja ne, mulkin tilas ba dimokraɗiyya ba.
“To idan za a yi adalci, zai yiwu a yanzu a rama wa Kiristoci abin da aka yi masu a 1984 da 1993?”
Kukah na nufin shin ko Musulmi za su yarda a yi shugaba da mataimakin sa duk Kiristoci?
Kukah ya ce shi fa ba haushin Tinubu ko Shettima ya ke ji ba. Ya ce basu da laifi.
“Ba laifin Tinubu da Shettima ba ne, laifin jam’iyya ce da ta ƙaƙaba wannan tsari. Jefa Tinubu cikin wannan ruɗani aka yi, shi da aboki na Kashim Shettima.”
Kukah ya ce ba za a fara ganin illar wannan tsari da APC ta shigo da shi don ta ci gaba da mulki ba, sai an fara kamfen gadan-gadan.
Ya ce a lokacin za a fara ganin illar abin, duba da yadda za a riƙa amfani da addini wajen kamfen tsakanin jama’a.
Ya ce tabbas wannan tsari da APC ta kawo ƙarƙashin mulkin Buhari, zai ƙara faɗaɗa giɓin bambance-bambancen da ke tsakanin mu a matsayin mazauna dunƙulalliyar ƙasa haɗa.
Ya ce tsari ne kawai da ‘yan siyasa su ka bijiro da shi domin su cimma burin su, amma ba su damu da irin illar da zai yi wa ƙasar da al’ummar ta ba.
Kukah ya shafe lokaci ya na sukar gwamnatin Buhari, wadda ya ce ta gaza ta fannoni da dama, kuma wajen dagula al’amurra, ba a taɓa yin gwamnatin da ta kai wannan ba.