2023: Sojoji na shan matsin-lambar neman su haɗa baki a yi murɗiya – Irabor, Babban Hafsan Tsaron Najeriya

A daidai lokacin da wasu ‘yan ta-kife ke ci gaba da banka wa ofisoshin INEC wuta a kudancin ƙasar nan, a Arewa kuma wasu manyan ‘yan siyasa na shelar sai sun ci zaɓe ko da tsiya-tsiya ko da tulin kuɗaɗe, wata sabuwa kuma ita ce iƙirarin da Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ya yi cewa ba tun yau ba, an daɗe ana yi wa sojoji da sauran jami’an tsaro romon kunne su haɗa baki a murɗe zaɓe.
Sai dai kuma Irabor ya ce sojoji tsaye su ke ƙyam a wuri ɗaya, a tsakiya, ba su goyon bayan kowace jam’îyya, kuma babu ruwan su da kowane ɗan takara.
“Tabbas a kowane zaɓe tun bayan dawowar mulkin dimokraɗiyya a 1999, sojoji na fama da matsin-lamba daga wasu ɓatagari marasa kishi, su na so sojoji su ba su ƙofar yin maguɗin zaɓe.
“Waɗannan marasa kishi ba wai a kan sojoji kaɗai su ka tsaya ba, har da sauran jami’an tsaro kamar su ‘yan sanda. To irin tsiyar su ke so a kowane zaɓe su riƙa tafkawa, mu kuma ba mu yarda da su.”
Irabor ya ce irin wannan matsin-lambar da sojoji ke sha ba za ta sare masu guiwa ba, sai ma ta ƙara masu kuzarin ƙara tashi tsaye wajen kare dimokraɗiyya.
Ya yi wannan bayani a wurin taron Ganawar Ma’aikatu da Manema Labarai karo na 61 da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa, wanda tawagar jami’an yaɗa labaran Shugaban Ƙasa ke shiryawa.
Irabor ya yi wannan kalami ne lokacin da ya ke amsa wata tambaya daga manema labarai, inda ya ke tabbatar masu cewa sojoji ba za su taɓa goyon bayan wata jam’iyya ko wani ɗan takara ba, kamar yadda su ke bisa wannan tsari tun daga dawowar mulkin siyasa a 1999.
“Na ji daɗi da har ku ka ƙara jaddada wannan gargaɗin ƙin daba kai borin masu neman sojoji su ba su haɗin ya hau, wanda Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ya yi. Na ji daɗin da ku ka ce ku na da damuwa. To amma mu dai tabbas duk inda gaskiya ta ke, to za a tsaya kan ta, kuma a fito da ita.
“Amma mu a ɓangaren sojoji, ai ba da ka mu ke aiki ba. A bisa tsari, ƙwarewa da kuma bin doka mu ke aikin mu. Kuma a haka za mu ci gaba da kasancewa.
Saboda haka daga yau ku daina nuna damuwa. Maimakon haka, ku ba mu amannar ku, ku gaskata wajen cika aikin mu bisa tsarin da doka ta gindiya, ba tare da bin ra’ayi ko son ran wasu ɓatagari ba.