2023: Mata 380 su ka fito takara a zaɓen Majalisar Dattawa da ta Tarayya – INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa an samu mace ɗaya tilo ta fito takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Hakan na ƙunshe cikin jerin sunayen da hukumar ta fitar a ranar Talata, mai ɗauke sa hannun Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye.
Ya ce an samu mata har 380 da za a fafata neman kujerun Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa da su.
A jerin sunayen an lissafa mata 92 masu neman kujerar Majalisar Dattawa, sai kuma wasu mata 288 da za a fafata neman kujerar Majalisar Tarayya da su.
A ɓangaren maza kuwa, INEC ta buga sunayen 1,008 masu neman kujerar Majalisar Dattawa, sai kuma wasu 2,832 da za su fafata neman kujerun Majalisar Tarayya.
INEC ta ce jam’iyyu 18 ne su ka shiga takarar zaɓen shugaban ƙasa, wanda za a fafata a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
“An samu masu takarar shugaban ƙasa da masu takarar mataimakin shugaban ƙasa har su 35 daga jam’iyyu 18. Akwai ‘yan takarar Majalisar Dattawa su 1,101, waɗanda a cikin su 92 mata ne. Sai kuma masu takarar Majalisar Tarayya su 3122.
“Za a yi takarar kujeru 109 a Majalisar Dattawa, sai kuma kujeru 360 a Majalisar Tarayya. Baki ɗaya kujeru 469 kenan.” Inji Okoye, wanda ya ƙara da cewa waɗannan ‘yan takara na majalisu sun zama 4,224 kenan.
Cikin waɗanda INEC ta wanke domin shiga takarar zaɓen Shugaban Ƙasa, har da Bola Tinubu na APC, Rabiu Kwankwaso na NNPP, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.
Sai dai kuma duk da jam’iyyar ADC ta dakatar da Kachikwu ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, sunan sa ya fito a cikin waɗanda za su fafata.
A jerin sunayen masu takarar Majalisar Dattawa dai babu sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan na APC da Machina wanda su ke tankiyar cancantar shiga takarar a tsakanin su.