2023: Atiku ya naɗa Shekarau, Saraki, Anyim masu bashi shawara na musamman

Ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya naɗa tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan Kwara, tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki masu bashi sharawa na musamman.
Haka nan kuma Atuku ya naɗa tsohon gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola, da tsohon shugaban jam’iyyar, Uche Secondus a matsayin masu bashi shawara daban daban a kamfen ɗin sa.
Ya naɗa tsohon shugaban majalisar Dattawa Pius Anyim a matsayin mai bashi shawara na musamman
Ranar Laraba ne za a fara Kamfen gadangaden a faɗin kasar nan.
Atiku Abubakar ne ɗan takarar shugaban Kasa na PDP kuma zai fafata ne da Bola Tinubu na Jam’iyyar APC, Peter Obi na LP, Rabiu Kwankwaso na NNPP da sauran ƴan takara na jam’iyyu.