Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 6 da cutar korona ta kashe a kasar nan.

Hukumar ta sanar da haka a shafinta na Facebook dake yanar gizo ranar likitin inda ta Kara da cewa cutar ta kashe wadannan mutane tsakanin ranar 22 zuwa 28 ga Disamba 2021.

Bayan haka NCDC ta bayyana cewa mutum 573 ne suka kamu da cutar a kasar nan ranar Litini.

Sannan daga cikin yawan mutanen da suka kamu da cutar an hada da yawan mutanen da suka kamu da cutar daga jihar Barno daga ranar 28 zuwa 31 ga Disemba 2021.

Zuwa yanzu mutum 243,450 ne suka kamu da cutar, an sallami mutum 215,352 da suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,039.

Mutum 25,111 na dauke da cutar a kasar nan.

Yaduwar cutar.

Legas – 95,168, Abuja-24,437, Rivers-13,232, Kaduna-10,213, Filato-10,027, Oyo-10,001, Edo-7,535, Ogun-5,496, Kano-4,768, Akwa-ibom-4,428, Ondo-4,662, Kwara-4,015, Delta-4,446, Osun-3,016, Enugu-2,824, Nasarawa-2,517, Gombe-2,695, Katsina-2,367, Ebonyi-2,048, Anambra-2,424, Abia-2,029, Imo-2,174, Bauchi-1,776, Ekiti-1,788, Benue-2,109, Barno-1,552, Adamawa-1,136, Taraba-1,254, Bayelsa-1,274, Niger-1,077, Sokoto-796, Jigawa-635, Yobe-501, Cross-Rivers-662, Kebbi-458, Zamfara-348, da Kogi-5.

A daidai ƴan Najeriya na kokarin kai komo wajen neman abin dasu saka a bakin salati, da kuma zaman dardar da ake yi na hare-haren ƴan bindiga da ya addabi mutane a Najeriya, hukumar NCDC ta bayyana cewa akwai yiwuwar sake garkame kasar nan idan aka ci gaba da samun yawan waɗanda suka kamu da Korona a kasar nan.

Shugaban hukumar NCDC, Ifedayo Adetifa,ya bayyan cewa Korona ta yi ƙamari yanzu a kasar nan akwai yiwuwar gwamnati ta ɗau sabbin matakai a kasar nan.

A karon farko tun barkewar Korona a watan Faburairun 2020 Najeriya ta samu sama da mutum 4000 da suka kamu da cutar a rana ɗaya
Ya ce gwamnati za ta iya daukan wannan mataki saboda yadda mutane suka yi watsi da matakan kariya da aka saka da suka haɗa da wanke hannaye, mulka man tsaftace hannaye, saka takunkumin fuska da yin nesa da juna, sannan kuma da rage cunkoso da taruka.

Sai dai kuma ba a nan ne gizo ke saka ba domin wasu kwararru da suka tattauna da PREMIUM TIMES game da wannan niyya ta gwamnati sun ce haka nan dai gwamnati za ta ci gaba da hakuri da mutane amma saka dokar zaman Kulle ba zai yiwuba a Najeriya yanzu ba.

Matsalolin da za a afka a ciki sun fi duk wani alfanu da za a samu idan aka garkame kasar.