Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Abdullahi Shehu ya angwance da ƴar Fim

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Abdullahi Shehu ya angwance da amaryarsa jarumar Kannywood Naja’atu Muhammad Suleiman wadda aka fi sani da “Murjanatu Ƴar Baba”.

An ɗaura auren nasu ne a yau bayan kammala Sallar Juma’a a Kano.

Ɗaurin auren ya zo bazata ba tare da sanarwa ba duk da yawan masoya da ɗan wasan ke da shi.

Shehu ya wallafa hoton amaryarsa a shafinsa na Instagram tare da rubuta “Alhamdulillah” ma’ana godiya ta tabbata ga Allah.

Hausa Daily Times ta ga shafukan manyan jaruman Kannywood na wallafa hotunan sabbin ma’aurata Abdullahi Shehu da Murjanatu suna taya su murnar aure.