Ƴan sanda sun damke wasu magidanta biyu masu shekaru 45 da 38 da suka yi wa ƴar shekara 13 fyaɗe a Jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta kama wasu magidanta biyu da take zargi da yi wa ƴar shekara 13 fyaɗe a karamar hukumar Kafin Hausa.

Mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP Lawan Shisu ya sanar da haka a wani takarda ranar Laraba.

Shisu ya ce mazajen biyu da suka kama na da shekaru 45 da 38 kuma dukkan su da ita yarinyar da suka yi wa fyaɗen mazauna karamar hukumar Kafin Hausa ne.

Ya ce rundunar ta kama mutanen ranar 1 ga Yuni.

Shisu ya ce wannan yarinya na karatu ne a makarantar ‘Special Primary’ dake Kafin Hausa.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin yanke musu hukunci a kotu.

A watan Mayu PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta saurari kararrakin fyade 35 a cikin watanni hudu.

Rundunar ta kuma saurari kararrakin fyade fiye da sauran laifuffuka kamar su garkuwa da mutane da kai wa mutane hari.

A cikin watanni hudu da suka gabata jihar ta samu raguwar wadanda aka yi garkuwa da su zuwa mutum 10 a cikin watanni hudun.

Rundunar ta yi kira ga iyaye da su rika sanya wa ‘ya’yansu ido da kula da zirga-zirgan su, musamman yara kanana da ake dora musu talla suna gararamba a tituna.