Ƴan bindiga sun sace malamai da ɗaliban Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Zariya

Rahotanni da sanyin safiyar Juma’a sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun dira Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin jihar Kaduna inda suka arce da wasu malamai biyu sannan suka kashe wani ɗalibi.

Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar Malamai Kwalejin Engineer Kofa, a wata ƴar gajeruwar takarda da ya raba wa manema labarai a Kwalejin ya ce maharan sun arce da malamai biyu sannan sun harbi wasu dalibai biyu.

Ɗaya daga cikin su mai suna Aliyu da ke karatun Statistics kuma yana ajin karshe ya rasu a asibiti, daya ɗalibin na kwance a na duba shi.

Wata malama a jami’ar, Hadiza Mohammed ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu ba a samu ainihin adadin yawan waɗanda suka bace tukunna domin ana ci gaba da bincike.

Sai dai sanarwar da ak fitar an ce wata mata da ƴaƴan ta biyu sun bayyana da safiyar Juma’a, bayan an sace su cikin dare.

Ta ce ko da yake ba ta zaune a cikin harabar Kwalejin dake UPE, tun a daren jiya ake gaya mata a waya cewa mahara sun dira makarantar kuma suna harbe harbe.

Ta kara da cewa ana nan ana ci gaba da yin bincike domin sanin yawan wadanda suka bace ba a gansu ba haryanzu.

Jihar Kaduna ta yi kaurin suna wajen hare-haren ƴan bindiga da yin garkuwa da mutane a yankin Arewa Maso Yamma.

A cikin watan jiya ne aka sako daliban jami’ar Greenfield da na kwalejin Gandun Daji dake Kaduna bayan sun shafe watanni tsare hannun ƴan bindiga.