Ƴan bindiga sun kashe mutum 49 a wani hari a jihar Sokoto

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Rahotanni daga jihar Sokoto sun ce ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar.

Wasu ganau sun tabbatar wa da BBC labarin inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma, yayin da mutanen ke cin babbar kasuwar Goronyon.

Mutanen waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu saboda tsaro sun ce ƴan bindigar sun afka wa kasuwar ne a yayin da ta cika makil da masu hada-hada daga sassan jihar da ma wasu yankunan.

“Ƴan fashin sun zo ne da misalin ƙarfe 4.30 zuwa biyar na yamma suka zagaye kasuwar suka buɗe wuta ta kowane ɓangare,” in ji ganau ɗin.

Ya ƙara da cewa “Mutane duk suka ruɗe wasu sun kwakkwanta a ƙasa don gudun harbin ya same su, yayin da wasu suka gudu amma masu tsautsayi sun rasa rayukansu.”

Ganau ɗin sun ce an ƙidaya gawa 49 yayin da mutum 17 suka jikkata kuma tuni an kai su asibitin a birnin Sokoto, “gawarwakin kuma an kai mutuwaren da ke babban asibitin garin Goronyo,” in ji ɗaya ganau ɗin.

Shaidun sun ce ƴan sandan kwantar da tarzoma da ƴan banga sun yi ƙoƙarin tarwatsa su amma ƴan fashin sun fi su yawa don haka suka kasa shawo kan lamarin.

“Daga baya jami’an tsaro sun je amma lokacin ƴan bindigar sun riga sun tafi,” in ji shaidun.