Ƙwace titin Abuja zuwa Kaduna da mahara su ka yi zai iya durƙusar da tattalin arzikin Najeriya -‘Yan Majalisa

‘Yan Majalisar Tarayya masu wakiltar Jihar Kaduna sun bayyana cewa hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a kan titin Abuja zuwa Kaduna zai iya zama babban bala’in da ka iya ruguza tattalin arzikin ƙasar nan.

Gamayyar ‘yan majalisar sun kira taron manema labarai ranar Alhamis, inda su ka nuna matuƙar damuwar su dangane da rashin tsaro kan titin Abuja zuwa Kaduna da ma sauran wasu manyan titinan faɗin ƙasar nan.

Ta kan titin Abuja zuwa Kaduna ne ake shigo da kayayyaki daga Lagos zuwa Kaduna, Kano, Katsina, Zamfara, Sokoto, Zariya, Jigawa da wasu garuruwa masu yawa a faɗin Arewacin ƙasar nan. Haka nan kuma ta wannan titi dai ne ake fita da kaya daga Arewacin Najeriya zuwa Abuja, Kogi, Kwara, Ondo, Ogun, Oyo, Osun, Ekiti, Lagos, Edo da sauran jihohin kudu da dama.

Honarabul Garba Datti, ɗan majalisar tarayya, kuma ɗan APC daga Kaduna, wanda shi ne shugaban gungun su, shi ya yi magana a madadin sauran.

Ya ce idan har ba a tashi tsaye an kawar da barazanar tsaro kan titin Abuja zuwa Kaduna ba, to matsalar za ta iya durƙusar da tattalin arziki.

Ya ce babban titi kamar na Abuja zuwa Kaduna, ba abin da gwamnatin za ta ƙi bayar da matsanancin kulawa ba ne a kan sa.

“Bai kamata gwamnati ta kauda kai kan babban titi kamar na Abuja zuwa Kaduna ba, ta bar shi a hannun ‘yan bindiga ba.”

“Titin nan shi ne babban titin da ya haɗe kudanci da Arewacin ƙasar nan, har ma da wasu maƙwautan ƙasashe na Afrika ta Yamma.

“Wannan titi shi ne babbar hanyar zirga-zirga, tafiye-tafiye da jigilar kayan kasuwanci a cikin faɗin ƙasar nan. Irin yawan motocin da ke karakaina kan titin ya nuna muhimmancin sa ga ƙasar nan baki ɗaya.”

Ya ce dukkan matakan samar da tsaron da aka girke a yankin, sun kasa biyan buƙatar samar da tsaro ne saboda ba ƙarfafa ba ne. Shi ya sa mahara ke komawa kan titin bayan ‘yan kwanaki da fatattakar su.”

Datti ya ce kisa, fashi da garkuwar da aka riƙa yi da mutane kan titin a cikin wannan makon abin ban-tsoro ne matuƙa, kuma bala’i ne ba ƙarami ba.”

Yayin da ya ke nuna jimamin kashe Tsohon Daraktan Hukumar FCDA, kuma ɗan takarar gwamna a jihar Zamfara, Hamisu Sagir, Datti ya ce ana yawan yin garkuwa da mutane a kan titin, amma kafafen yaɗa labarai ba su bugawa, saboda ba da masaniyar an yi.