ƘUNCIN RAYUWA: Tsadar kayan abinci ya ƙara tsere wa talaka fintinkau cikin Nuwamba -FAO

Hukumar Bunƙasa Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), ta ce kayan abinci ya ƙara tsada a duniya sosai a cikin watan Nuwamba.

FAO ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin da rabon da ya yi irin sa farat ɗaya, tun cikin 2011.

A Najeriya lamarin ya zo wa talakawa a daidai lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da hana manoma kwasar amfanin gona tare da hana su yin noman.

Sannan kuma tsadar kayan abincin talaka ta ke shafa, wanda baya ga haddasa masa gudun hijirar tserewa daga Boko Haram ko ‘yan bindiga, gwamnatin ƙasar na shirye-shiryen nunka kuɗin man fetur.

Tsadar kayan abinci a duniya ya faru ne kwanan nan, saboda bijiro da buƙatar alkama da madara da dangogin ta.

Haka dai Hukumar FAO ta bayyana a jadawalin Farashin Kayan Abinci, wanda ta fitar a ranar Alhamis.

Farashin kayan abinci ya na bisa ma’aunin ɗigo 134.4 a watan Nuwamba, yayin da kenan ya ƙaru da kashi 1.2 daga watan Oktoba. Sannan kuma da kashi 27.3 a watan Nuwamba na shekarar 2020.

“Tsadar kayan abinci a cikin Nuwamba shi ne tashin farashin kayan abinci sau huɗu kenan a jere, a kowane wata. Haka FAO ta bayyana, tare da cewa mizanin tsadar ya yi tashin rabon da ya yi irin sa tun cikin shekarar 2011.
Ƙarancin ruwan shuka da canjin yanayi a ƙasar Austaraliya ya haifar da rashin wadataccen kayan abinci irin wanda aka saba girbewa a kowace kaka.

Rahoton ya ce farashin masara ya yi sama a cikin watan Nuwamba, saboda kasuwar ta daga Ajentina, Brazil, Yukharain da Amurka.

Sauran kayayyakin da su ka ƙara kuɗi sun haɗa da madara, sukari, man girki, nama da waken soya, man da ake sarrafawa daga rake da sauran kayan gona.

Fargabar sake ɓarkewar cutar korona nau’in ‘Omicron’ da a yanzu ta ɓarke a ƙasashe 26, iya ma ta firgita farashin kayan abinci har ya yi tashin da ta fi ƙarfin talaka.

Wani rahoto da BBC ta buga a ranar Alhamis ta ce a yanzu ƙasar da ta fi kowace tsadar rayuwa a duniya, ita ce Isra’ila, sai Singapore, sannan sai Faransa.

Sai dai kuma irin waɗannan ƙasashen, da wahala a iya gane tsadar abinci na samun su, saboda ƙarfin aljihun ‘yan ƙasar na da nauyin da zai iya sayen kayan abincin a farashi mai tsada.

Saɓanin Najeriya, inda yawanci talakawan ƙasar da aka ƙiyasta sama da miliyan 82, ba kowane ke iya samun naira 1,500 a rana ɗaya ba.

Matsalar tsaro a Najeriya ta tilasta kulle wasu kasuwannin garuruwa da dama a Katsina, Zamfara, Sokoto da wasu sassan jihar Kaduna.

Wannan lamari tare da kulle kan iyakokin ƙasar na ya ƙara haddasa hauhawar kayan abinci a Najeriya.p