ƘIDAYA: Wani Basarake yayi taron faɗakar da al’ummar sa kan shirin shata iyakoki a Katsina

Kanwan Katsina kuma Hakimin Ketare dake Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina, Alhaji Bello Usman, ya gudanar da taron wayarwa al’ummar yankinsa kai, domin tabbatar da an samu nasarar shirin lissafi da shata iyakoki na gundumomi a Jihar Katsina.

Hakimin yayi wannan kiran ne a sa’ilin da yake taro da Dagattai a fadarsa dake Ketare, inda ya bukacesu dasu bayar da goyon baya a shirye-shiryen da ake yi na gudanar da Kidayar Al’umma da za’ayi a fadin Kasar.
Kankara, ya umarci Dagattai da Shuwagabannin Addini dake yankin, dasu yi amfani da San kira da kuma Hudubobi a Masallatai, domin fadakar da Mabiyansu akan mahimmancin shirin, wajen cigaban Kasa da kuma tsare-tsaren tattalin arziki.
Yace Shirin zai dora gwamnati akan hanya a yayin gudanar da tsare-tsaren da za tayi na gina hanyoyi, da cibiyoyin kula da Lafiya da ilimi gami da sauran ababen more rayuwa.
Daganan Basaraken ya bukaci Al’ummar yankin, dasu baiwa ma’aikatan da zasu gudanar da aikin shata iyakokin damar zuwa inda suke bukata ba tare da yi masu iyaka ba a lokacin shirin, tare da basu ingantattun bayanai game da adadin abubuwan da suke bukata domin shata gidajen su.
Ana dai sa ran shirin zai shafe tsawon wata daya ana gudanar dashi.