ƘARA WA BARNO DAWAKI: An danƙara wa ɗan Shugaban SSS kyautar danƙareren gidan naira miliyan 90 a Abuja

A karon farko a Najeriya, an yi wa ɗan wani babban jami’in gwamnatin tarayya danƙareriyar kyautar danƙareren gida.

An bayar da kyautar gidan ga Abba Yusuf Bichi, ɗan Babban Daraktan Hukumar ‘Yan Sandan Leƙen Asiri (SSS) na ƙasa.

An danƙara masa kyautar gidan mai ɗakuna biyar a yankin Rukunin Gidaje na Hilltop Estate da ke Apo, a Abuja.

Kamfanin Gina Rukunin Gidaje na Titan Network, a ƙarƙashin BSTAN Group, waɗanda ke harkokin haɗakar aikin gona da sauran hada-hada ne su ka bada kyautar gidan.

An bayyana kyautar a lokacin da ake ƙaddamar da Yusuf matsayin Jakadan Kamfanin Titan Network.

Babbar Daraktar Titan Network, Becky Olubukola ce ta fara sanar da batun bayar da kyautar a shafin ta na Instagram, ta ce “sun ɗauki matashin ɗan ƙwallon a matsayin jakadan inganta rayuwar matasa da kuma jaddada haɗin kan Najeriya.”

Olubukola ta ce Bichi yaro ne ɗan ƙwallon da bai kai shekaru 20 ba, kuma ya ke wasa a ƙungiyar KV Mechelen ta Belgium.

“Mun zaɓe shi jakadan kamfanin mu saboda yaro ne da ya yi amnana da kishin Najeriya da ƙwazon son ganin ƙasar nan ta bunƙasa.

Bichi ya ce wannan kyauta da aka ba shi, to tamkar matasan Najeriya ne gaba ɗayan su aka bai wa kyautar.

Idan ba a manta ba, Abba Bichi ya ragargaji EFCC cikin watan jiya, saboda sun kama mutumin nan mai tashen ɓarusa da daƙasharama da kuɗaɗen fitar hankali, Obi Cubana.

Bichi cewa ya yi kama shi zalunci ne. EFCC ta kama shi bisa zargin walle-walle.