Ƙaddamar Da Littafin Daular Usmaniyya: Na so na halarta, amma tsoron ‘yan bindiga ya hana ni zuwa -Murry Last, marubucin littafin

Marubucin ‘The Sokoto Caliphate’ wanda PREMIUM TIMES ta ƙaddamar s ranar Talata, ya nuna takaicin halartar taron daga Amurka.

A jawabin sa da aka nuno shi kai-tsaye a zauren taro ya na gabatarwa ta intanet daga gida, Last ya ce ya yi farin cikin ganin an sake buga littafin.

Sai dai kuma ya nuna rashin jin daɗin halartar da bai yi ba, inda ya ce ya na tsoro kada ‘yan bindiga su yi garkuwa da shi ne a Arewacin Najeriya.

A yau ne aka ƙaddamar da littafin a Cibiyar Gudanar da Taruka ta ‘Yar’Adua Centre, a Abuja.

Murray Last: A Saida Rai A Nemo Suna:

Murray Last ya rubuta littafin shekaru 54 da suka gabata, a lokacin da ya ke karatun digirin-digirgir Ph.D a Jami’ar Ibadan.

Littafin Daular Usmaniyya (Daular Sakkwato), shi ne sahihin littafi mafi inganci mai ɗauke da tarihin yadda aka gudanar da mulkin Daular Sakkwato daga 1804 zuwa 1903.

Ya shafe tsawon lokaci ya na bincike a Sokoto a lokacin da ya ke aikin tattara bayanan littafin na sa.

Murray Last Bature da masanin rayuwar Hausawa da al’ummar ƙasar Hausa ciki da bai.

Mashahurin mai bincike ne wanda ya taɓa shafe shekara ɗaya cur a cikin wani ƙauye a Jihar Kano, inda ya yi cikakken binciken yadda Maguzawa ke rayuwar su.

“Ba zuwa na riƙa yi ina komawa cikin Kano ba. A cikin ƙungurmin daji cikin gidan wani Bamaguje aka gina min ɗaki na daban. Kuma ban-ɗaki na daban.

“To a can na zauna ina bincike na da yawace-yawacen tattara bayanai, har na shekara ɗaya.”

Haka ya bayyana wa wakilin mu wanda a shekarun baya ya taɓa tattaunawa ta musamman da shi, cikin 2010 a Kano.

Ba a nan kaɗai Last ya tsaya ba. A cikin Kano kuwa, Murray Last ya karaɗe birnin kakaf a wurin binciken-ƙwaƙwaf ɗin sanin “ranar da Hausawa su ka fi mutuwa.”