Ƴan Tiwita sun ce ba za su zaɓi Atiku ba saboda ya goge sakon yin tir da kisan Deborah da ta yi Ɓatanci ga Annabi

Masu rubuce-rubuce a shafin tiwita da dama sun bayyana rashin jin daɗin du ga goge sakon yin tir da kisan Deborah ɗalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu ɗalibai na kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake Sokoto suka kashe wata ɗaliba da ake zargin ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.
A sakon da daliban ta saka ta yi kakkausar suka ga Annabi SAW wanda hakan ya fusatar da wasu daga cikin ɗaliban makarantar har ya kai ga sun kashe ta da jifa.
Mutane da dama sun yi tir da kisan Deborah sai dai kuma wasu da dama na ganin marigayiyar ta yi ganganci mai tsadar gaske.
Masu karatu da rubutu a tiwita suna korafin goge sakon da Atiku ya rubuta suna mai cewa yana nufin kenan shima ya na tare da kisan da aka yi wa Deborah kenan.
Tuni dai gwamnati Sokoto ta saka a gudanar da bincike akai sannan kuma gwamnati ta yi kira ga mutane su kwantar da hankulansu a zauna lafiya da juna.
Rundunar Ƴan sandan jihar Sokoto ta sanar da kama wasu mutum biyu cikin waɗanda ake zargin suna da hannu wajen jifar wannan yarinya har ta sheka lahira.