Ƴan sanda sun hallaka wasu manyan kwamandojin IPOB

Rundunar ƴan sanda ta ce takai wani samame sansanin ƴan ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar biyafara dake fito na fito da gwamnati.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Imo CSP Michael Abattam, ya ce wannan wata na sara ce ta yunkurin magance ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya a yankin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sansanin yana hayin Amaifeke a ƙaramar hukumar Orlu ta jihar Imo.

Ƴan sanda sun hallaka wasu manyan kwamandojin IPOB
Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗaliban makarantar Sakandare da aka sace a Zamfara sun kubuta

Abattam ya ce sun samu cikakken bayanin sirri kan cewa waɗannan mutanen na zaune a wani gida da ba a kammala gininsa ba a yankin, kuma suna yunƙurin ƙara ƙaddamar da hare-harensu kan ƴan sanda da sauran gine-ginen gwamnati..
” ‘yan sanda sun kai wa mambobin kungiyar ‘yan ta’addan hari a maboyarsu tare da bude musu wuta, in ji sanarwar da Abattam ya fitar a ranar Asabar.
“An samu nasarar kashe wasu mambobinsu uku a wannan hari.”

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 13, 2021 9:22 AM