Ƴan bindiga sun saki daliban makarantar Yawuri a Jihar Kebbi

Yan Bindiga sun saki wasu daga cikin daliban kwalejin makarantar Gwamnatin Tarayya dake aYawurin Birnin Kebbi yau Alhamis.

Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito yadda Yan Bindigar suka arce da daliban a ranar 17 na watan Yuli a harabar makarantar dake a garin Yauri.

Yahaya Sarki, Kakakin gwamna Atiku Bagudu shi ne ya tabbatar wa manema labarai sakin daliban a yammacin yau Alhamis saidai yace wasu ne daga cikin daliban aka sako kuma gwamnati tana kokarin ganin cewa a sako raguwar daliban.

A yanzu daliban sun iso Babban Birnin Kebbi, kuma ana kokarin duba lafiyarsu kafin daga bisane a sadasu da iyalinsu.