Ƴan bindiga sun sace Sarkin Bunguɗu a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Ƴan bindiga sun buɗe wa tawagar motocin sarkin Buguɗu, Maimartaba Hassan Attahiru a Hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Jaridar Daily Nigerian wacce ta wallafa labarin ta bayyana cewa maharan sun buɗe wa motocin sarkin wuta ne da dole suka tsaya daga nan kuma suka sace shi.

Majiya ta shaida wa jaridar cewa ƴan bindigan sun ritsa da basaraken ne a daidai kamfanin Olam da bai wuce kilomita 30 zuwa garin Kaduna ba.