Ƴan bindiga sun dasa bama-bamai a hanyar jirgin ƙasa Abuja-Kaduna

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa, NRC, a ranar Alhamis ta tabbatar da fashewar wani abin fashewa ga ɗaya daga cikin jiragenta da ke jigila a hanyar Kaduna zuwa Abuja, wanda wasu da ba a san ko su waye ba suka dasa akan haryar jirgin.

Manajan darakta na NRC, Fidet Okhiria, wanda ya zanta da Jaridar Tribune Online, ya bayyana cewa abubuwan fashewar sun lalata hanyoyin jirgin ƙasan a wani wuri tsakanin ƙauyen Dutse da Rijana.

  • Ƴan bindiga sun dasa bama-bamai a hanyar jirgin ƙasa Abuja-Kaduna
  • Wa ya ɗirkawa ƙannen sa uku mata ciki

Sai dai ya ce suna ci gaba da ƙoƙarin ganin an dawo da ayyukan jirgin ƙasa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja,”

Ya kuma tabbatar da cewa babu harbin bindiga ga jirgin kamay yanda ake yayatawa.

Sai dai wasu majiyoyin sun ce an buɗawa jirgin wuta a daren jiya Laraba kafin tashiwan abin fashewa na safiyar Alhamis.

“Yan bindigan sun fara kai farmaki kan jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna mai lamba AK9 tsakanin Rijana da Dutse. An yi ta harbin jirgin, amma ya yi ta kokarin tafiya har na kusan kilomita 7 kafin ya tsaya domin harbe -harben ya lalata tankin mai, ”wani ma’aikacin Kamfanin Jirgin Ruwa na Najeriya, NRC kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

“A lokacin da aka kai harin, jirgin ƙasa ya kasa tuntubar tashar Abuja. Sai bayan awanni kafin aka samu yin magana da tashar sannan suka turo jirgin da zai kawo ɗauki da tsakar dare.

“Da safiyar yau kuma, wani jirgi mai lamba KA2 da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja shi ma ya yi nasarar tsallake hanyoyin jirgin da suka karye, bayan an dasa masa abubuwan fashewa, cikin ikon Allah ya isa Abuja.”

Tsohon Sanata daga Kaduna, Shehu Sani wanda yana daga cikin fasinjojin jirgin ya tabbatar da faruwan haka a shafinsa na Facebook a safiyar yau.