ƘALUBALEN MAWAƘAN ZAMANI NA HAUSA: Davido zai raba naira miliyan 250 da ya tara rana ɗaya ga gidajen marayun ƙasar nan

Fitaccen mawaƙin Kudu ɗan Legas David Adeleye, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa zai raba naira miliyan 201 da ya samu a cikin kwanaki biyu ga gidajen marayun faɗin Najeriya.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a 19 Ga Disamba, Davido ya ce shi dama bai yi niyyar yin amfani da kuɗin ba.

“Har a zuciya ta dama na yi niyya ne na raba kuɗaɗen a gidajen marayu, bikin murnar zagayowar ranar haihuwa ta.

“Saboda haka ina sanar da cewa waɗannan kuɗaɗe da masoya na suka tara min har naira miliyan 201, ni kuma na ƙara miliyan 50 a kai, zan haɗa duk na raba su a gidajen marayun ƙasar nan.”

Davido ya gode wa ɗimbin masoyan sa da suka tura masa gudunmawar kuɗaɗe.

Tun da farko dai Davido ya shiga shafin sa na Tweeter, inda ya yi sanarwar neman gudummawar kuɗaɗe har naira miliyan 103 domin ya biya kuɗin harajin kwastan, na wata motar da ya ce ya sayo daga waje, amma ta na hannun kwastan sai ya biya kuɗin haraji tukunna.

A rana ɗaya an haɗa masa kusan Naira miliyan 160.